Trump Ya Sanar da Cafke Shugaba Maduro Bayan Hare-haren Amurka a Venezuela Mai Arzikin Man Fetur
Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanar a ranar Asabar, 3 ga Janairu, 2026, cewa sojojin Amurka sun cafke shugaban ƙasar Venezuela, Nicolás Maduro, tare da matarsa Cilia Flores.
Sanarwar ta biyo bayan jerin hare-haren sama masu faɗi da aka kai kan wuraren soji da muhimman cibiyoyi a birnin Caracas, babban birnin ƙasar.
Rahoton Okay News ya ce Shugaba Trump ya bayyana cewa aikin wani haɗin gwiwa ne tsakanin sojojin Amurka da hukumomin tsaron cikin gida, inda aka kama shugaban Venezuela tare da fitar da shi daga ƙasar.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce: “Ƙasar Amurka ta yi nasarar kai babban hari a Venezuela da shugabanta… ƙarin bayani na nan tafe.” An shirya gudanar da taron manema labarai da ƙarfe 11:00 na safe (EST) a gidan Shugaban ƙasar da ke Mar-a-Lago.
Hare-haren sojin sun fara ne da sassafe, inda aka ji fashe-fashe kusan lokaci guda a manyan sansanonin soji.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa Fuerte Tiuna, babbar hedikwatar sojin Venezuela, da kuma La Carlota, muhimmin filin jirgin saman soji, na daga cikin wuraren da aka fi kai wa hari.
Mazauna birnin Caracas sun bayyana yanayin a matsayin mai matuƙar firgici, inda suka ce karar fashe-fashen ta fi ƙarar tsawa ƙarfi, tana sa gine-gine rawar jiki, tare da hayaki mai kauri baki ya turnuke sararin samaniya.
Rahotanni sun nuna cewa yankuna da dama sun rasa wutar lantarki, yayin da aka ga jiragen yaƙi masu saukar ungulu na soji suna shawagi a sama da fadar shugaban ƙasa.
Venezuela Ta Ayana Dokar Ta-Baci
Kafin bayyanar rahotannin cafke shugaban ƙasar, gwamnatin Venezuela ta fitar da sanarwa inda ta yi Allah-wadai tare da yin tir da abin da ta kira hare-haren mulkin mallaka na soja.
Rahotanni sun ce Shugaba Maduro ya sanya hannu kan wata doka da ta ayyana halin rikicin waje a duk faɗin ƙasar, tare da bayar da umarnin aiwatar da dukkan tsare-tsaren kare ƙasa.
Jami’an Venezuela sun yi ikirarin cewa hare-haren wani yunkuri ne na ƙwace muhimman albarkatun ƙasar, musamman arzikin man fetur da ma’adanai.
Sun kuma yi kira ga ƙungiyoyin jama’a da dakarun sa-kai da su tashi tsaye domin kare ƙasar.



