Ƙungiyar Northern Minority Forum Ta Ce Dogara Na Neman Dawo Da Tasirinsa Gabanin Zaɓen 2027
Ƙungiyar Northern Minority Consultative Forum (NMCF) ta zargi tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, da yunƙurin neman dawowa sahun tasiri a siyasa gabanin zaɓen 2027, ta hanyar abin da ta kira kalamai masu rarrabawa da ruɗarwa.
Shugaban ƙungiyar, Daure David, ya bayyana hakan yayin ganawa da ’yan jarida a Abuja ranar Litinin.
Ya yi ikirarin cewa Dogara ya yi aiki a kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, kuma a yanzu yana ƙoƙarin sake jan hankalin jama’a ta hanyar tayar da muhawara kan rabon madafun iko da addini.
Ƙungiyar ta ƙaryata jita-jitar da ke cewa Shugaba Tinubu na iya sauya Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da ɗan takarar Kirista daga Arewa a 2027, tana mai bayyana irin waɗannan rahotanni a matsayin “haɗari, ruɗarwa, kuma masu manufa ta siyasa.”
Daure David ya ce makamancin irin waɗannan jita-jita sun taɓa yawo a baya cewa za a naɗa Dogara a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), amma hakan bai taɓa faruwa ba.
Ƙungiyar ta kuma soki goyon bayan wa’adin mulki na biyu da wasu tsofaffin ’yan majalisa suka nuna wa Shugaba Tinubu a taron National Forum of Former Legislators (NFFL) na 2026, tana cewa goyon bayan ya samo asali ne daga muradin kai ba ci gaban ƙasa, haɗin kai da zaman lafiya ba.
Sai dai ta bayyana damuwa kan yadda tsofaffin ’yan majalisa 17 suka nesanta kansu daga wannan goyon baya daga baya, lamarin da ta ce wasu ’yan siyasa ke amfani da shi wajen haddasa ruɗani a cikin jam’iyyar APC.
Dangane da kalaman Dogara a shirin Sunday Politics na tashar Channels Television, inda ya yi kira da a tabbatar da adalci da haɗa kowa wajen rabon iko, ƙungiyar ta zarge shi da ɓoye muradinsa na siyasa a ƙarƙashin neman daidaito.
Daure David ya ce, “Waɗannan kalamai ba don adalci ko addini ba ne, illa neman dawo da tasiri.”
Ƙungiyar ta kuma yi zargin cewa Dogara ya yi kamfen a kan tikitin Musulmi da Musulmi na APC a tsakanin Kiristoci a zaɓen 2023.
Ta tambayi dalilin sukar gwamnatin Tinubu da Shettima, tana cewa har yanzu ba a fayyace abin da ke damun tafiyar da gwamnati ko amfanin da ta kawo wa Musulmi da Kiristoci a faɗin ƙasar nan ba.
Ƙungiyar ta gargaɗi cewa amfani da addini a matsayin makamin siyasa gabanin 2027 na iya zama kuskure mai tsanani, wanda zai iya jawo asarar goyon baya musamman a yankin Arewa maso Gabas.
Ta kare Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, tana bayyana shi a matsayin mataimaki mai biyayya da jajircewa a aikinsa.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa Dogara ba shi ne jigon haɗin kan Arewa maso Gabas ba, tana mai zargin cewa ya mara wa Atiku Abubakar baya a zaɓen 2023 bayan ya kasa samun matsayin mataimakin shugaban ƙasa.
A ƙarshe, ƙungiyar ta yi gargaɗi cewa duk wani yunƙuri na amfani da ƙananan ƙungiyoyin addini ko ƙabilu don cimma muradin siyasa na iya raba jam’iyyar APC tare da jefa makomarta a zaɓen 2027 cikin haɗari.




