Mataimakin Gwamnan Bauchi Ya Jagoranci Taron Nada Kwamishinan Kuɗi ‘Wazirin Giade’
An naɗa Kwamishinan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki na Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, da sarautar gargajiya ta Wazirin Giade, a matsayin girmamawa bisa gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa harkokin al’adu da ƙarfafa cibiyoyin gargajiya a jihar.
An ba shi sarautar ne a lokacin wata ziyarar girmamawa da Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Auwal Jatau, ya jagoranta tare da wasu masu ruwa da tsaki da kuma sarakunan gargajiya daga Karamar Hukumar Giade.
Mambobin tawagar sun bayyana cewa an yanke shawarar ba da sarautar ne sakamakon irin goyon bayan da Yakubu Adamu ke bai wa harkokin gargajiya, da kuma rawar da yake takawa wajen haɗa kai tsakanin gwamnati da al’umma domin ci gaban yankunan karkara.
Sun kuma jaddada cewa haɗin gwiwa tsakanin jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya na da muhimmanci matuƙa wajen samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban al’umma a matakin ƙasa.
Da yake mayar da martani, Yakubu Adamu ya nuna godiyarsa ga Mataimakin Gwamna, Majalisar Gargajiyar Giade da dukkan mambobin tawagar bisa wannan girmamawa da aka yi masa.
Ya bayyana cewa sarautar ba kawai karramawa ba ce, illa nauyi da alhaki, inda ya sha alwashin ci gaba da mutunta sarakunan gargajiya da kuma tallafa wa duk wani yunƙuri da zai kawo ci gaba ga al’ummar Giade da Jihar Bauchi gaba ɗaya.
An kammala ziyarar da addu’o’in neman zaman lafiya, haɗin kai da dorewar ci gaba a Karamar Hukumar Giade da Jihar Bauchi baki ɗaya, yayin da jihar ke bikin cika shekaru 50 da kafuwarta.
Ga Hotuna Daga Bisani







