LabaraiSiyasa

Gwamnan Bauchi ya yafewa fursunoni 73, ya kuma ba su tallafin Naira miliyan 7.3 don sabuwar rayuwa

Daga Samuel Luka, Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi afuwa ga fursunoni 73 daga cibiyoyin gyaran hali daban-daban a jihar, tare da ba kowane daga cikinsu tallafin Naira 100,000 domin taimaka musu su koma cikin al’umma.

An gudanar da bikin bayar da afuwar ne a dakin taro na Banquet Hall da ke gidan gwamnatin jihar Bauchi, inda gwamnan ya ce an yi hakan ne a daidai lokacin watan Ramadan, wanda ya bayyana a matsayin lokaci na rahama da tunani a kan rayuwa.

Da yake jawabi a ranar Laraba, gwamnan ya ce ikon yin afuwa wata amana ce mai muhimmanci da ke bukatar hikima da taka-tsantsan wajen aiwatar da ita.

“Ramadan wata ne na rahama, tunani, tuba da sabunta alaka da Ubangiji,” in ji shi.

Ya kara da cewa, duk da cewa adalci yana tabbatar da tsari a cikin al’umma, rahama kuma na dawo da fata ga mutane.

Gwamnan ya bayyana cewa an dauki matakin yafewa fursunonin ne bayan nazari mai zurfi, inda aka duba abubuwa da suka hada da nadama, sauyin halayya mai kyau, yanayin lafiya, shekaru da kuma abin da zai amfani al’umma baki daya.

Ya ce matakin ba wai alama ce kawai ba, illa wata dama ce da ake bai wa wadanda suka cancanta domin su fara sabuwar rayuwa.

Gwamnan ya kuma gode wa Babban Lauyan jihar da kuma kwamitin da ke ba da shawara kan ikon afuwa, tare da Nigerian Correctional Service, bisa rawar da suka taka wajen gudanar da aikin cikin gaskiya da tsari.

Ya ce tallafin Naira 100,000 da aka ba kowanne daga cikin wadanda aka saki zai taimaka musu wajen sake tsayawa da kafafunsu a cikin al’umma.

A nasa bangaren, shugaban Nigerian Correctional Service a Bauchi, Monday Tebu, ya gode wa gwamnan bisa wannan mataki, tare da rokon al’umma da su karbi wadanda aka saki domin taimaka musu su koma rayuwa ta gari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button