LittafiLabarai

SAFIYA PART 2 Story | Text & Video

SAFIYA PART 2 Story Text Video

Watch Safiya 2 Story Video Download Below;

KARANTA SAFIYA PART 2 TEXT

Salati ɗaya daga bakin direba ya mayar da tafiyar Abuja zuwa mafarkin da Safiya ba za ta taɓa mantawa da shi ba.
Daga nesa, direban ya hango mutane ɗauke da bindigu a tsakiyar hanya.
Wasu mutane suna kwance a ƙasa, motocinsu a gefe.
Ya taka birki da ƙarfi.
Safiya ta ɗaga kai.
“Innalillahi!”
Hussaina ta kama hannunta, jikinsu ya fara rawa.
Masu bindigar suka fara rugowa wajen motar su Safiya.
Safiya ba ta jira komai ba.
Ta buɗe ƙofa ta fita da gudu cikin daji.
Ɗaya daga cikin mutanen ya biyo bayanta.
“Keh Ki tsaya! Kona harbe ki!”
Safiya ta ƙara gudu.
Takalmin ta ya tsinke.
Ƙaya suka yage mata kaya, ƙafafunta suka fara zubar da jini saboda kananan duwantsun da take takawa.
Amma tsoro ya hana ta jin ciwo.
Bayan dogon gudu, mutumin ya tsaya ya koma wajen sauran.
Ashe masu garkuwa da mutane ne.
Sun kama Hussaina da direban.
Safiya kuwa tayi gudu har kusan awa biyu kafin ta faɗi a gindin wani dutse.
Kishirwa ta addabe ta.
Amma abin da ya fi kashe mata zuciya shi ne tunanin Hussaina.
“Ya Allah… me suke yi mata yanzu?”
Ta kwana a wurin cikin sanyi, yunwa da tsoro.
Da gari ya waye, ta tashi ta ci gaba da tafiya.
Ba ta san inda za ta je ba.
Kuma bazata iya komawa gida ba.
Me za ta gaya wa iyayen Hussaina?
Sun yi bankwana da kawayensu cewa Abuja za su je su dawo da iPhone.
Yanzu Hussaina tana hannun masu garkuwa.
Chan sai Safiya ta hango wani manomi yana aikin gona da tractor.
Ta nufe shi.
“Slm Ranka ya daɗe…”
Ya kalle ta cikin mamaki.
“Me ya same ki? Ina kika fito?”
Sai Safiya ta ɓoye masa gaskiya.
“Na ɓata hanya ne. Ni ’yar Abuja ce.”
Mutumin ya tambaye ta wasu ’yan tambayoyi, sannan ya ce:
“Ki zo muje gidana ki huta. Gobe zan nemo wanda zai kai ki cikin gari.”
Safiya tadan yi jinkiri.
Tun daga farko zuciyarta ba ta amince da shi sosai ba.
Amma yunwa, kishirwa da gajiyar da take ciki suka sa ta bi shi.
Da suka isa gidan, sai Safiya ta fahimci cewa mutumin yana zaune shi kaɗai.
Babu mata.
Babu yara.
Ya ba ta abinci da ruwa.
Safiya ta ci sai ta ji jikinta ya fara samun ƙarfi.
Daga baya ya ce:
“Ki kwana anan. Gobe za mu nemi yadda za ki koma gida.”
Saboda babu inda za ta je, Safiya ta amince.
Dare ya yi.
Gidan ɗaki ɗaya ne kacal.
Safiya ta kwanta a gefe, mutumin kuma ya kwanta a ɗayan gefen.
Amma duk da gajiyar da ke jikinta, barci ya gagare ta.
Wani abu a zuciyarta yana gaya mata kada ta yi masa cikakken yarda.
Chan cikin dare sai ta ji motsi.
Ta buɗe ido a hankali.
Mutumin ne yake matsowa kusa da ita.
Ta ja baya.
“Me kake yi?”
Bai amsa ba.
Sai ya miƙa hannu ya fara taɓa ta.
Safiya ta ture shi da ƙarfi.
“Kada ka sake taɓa ni!”
A wannan lokacin ne tsoron da ta ji masa tun farko ya zama gaskiya.
Ta fahimci cewa saurin taimakon da ya yi mata bawai tausayinta yaji ba amfani yakeso yayi da ita.
Ta miƙe da sauri ta nufi ƙofar.
Mutumin ya ce:
“Ki kwanta mana…”
Safiya ta buɗe ƙofar ta fita cikin duhu.
Ta gudu daga gidan manomin cikin duhun dare, ba tare da ta san inda za ta dosa ba.
Ba ta san garin da take ba.
Ba ta da waya.
Ba ta da kuɗi.
Kuma babu wanda ta sani a kusa da ita.
Har zuwa kusan ƙarfe biyu na dare, chan ta hango wani babban trailer yana tahowa.
Ta tsaya tsakiyar hanya tana daga hannu.
Sai direban ya tsaya ya ɗauke ta.
Da ta shiga, Safiyya ta ba shi cikakken labarin abin da ya faru, daga tafiyarsu da Hussaina, har zuwa inda masu bindigar da suka tare su da kuma gidan manomin da ta gudu daga ciki.
Ta yi kuka tana cewa:
“Wataƙila karyanda nayiwa mahaifina cewa zamuje biki Kano neh abubuwan nan suketa faruwa dani.”
Direban ya gaya mata cewa hanyar Abuja tana da masu garkuwa da mutane masu hatsari.
“Idan ba su kashe Hussaina da direban ba, to tabbas za a nemi kuɗin fansa mai yawa kafin a sake su.”
Da safe suka isa Abuja.
Sai Safiya ta fahimci girman matsalarta.
Ba ta da waya.
Ba ta da lambar mutumin da suka zo Abuja domin ganawa.
Ba ta san adireshinsa ba.
Kuma ba ta san kowa a Abuja ba.
Dashike kusada tashan mota direban tirelan ya sauketa
Tana tsaye cikin ruɗani sai wani mutum ya matso kusa da ita.
“Safiya?”
Ta juya da sauri.
Mutumin ya ce:
“Na san ba ki da inda za ki je. Zan iya kai ki wajen mutumin da kika zo Abuja domin ki gana dashi.”
Safiya ta yi shiru.
“Ta yaya ka san wanda nake nema?”
Mutumin ya yi murmushi.
“Ki zo kawai. Za ki samu abinci, wuri ki huta, sannan za mu magance komai.”
Sai yakama hanya yaje ya buɗe ƙofar motarsa.
Safiya ta kalli motar.
Ta kalli mutumin.
Sai ya ƙara da cewa:
“Ko ki tsaya nan ki jira waɗanda suke neman ki su same ki.”
Wannan magana ta sa Safiyya ta firgita.
Domin ba ta taɓa gaya masa cewa akwai mutanen da suke nemanta ba.
Ta koma baya.
Sai mutumin ya furta abu na ƙarshe:
“Hussaina ta riga ta gaya mana komai game da ke.”
Safiya ta daskare.
Hussaina tana hannun masu garkuwa… ko kuma tana cikin wannan shirin tun farko?
Ci gaba a Part 3…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button