LabaraiLittafi

SAFIYA PART 1 Story [Text & Video Download]

SAFIYA STORY PART 1 Text & Video Download

Watch Safiya Story Part 1 Below;

KARANTA LITTAFIN SAFIYA

Safiya ta yi tunanin tafiyar Abuja za ta sa ta dawo da iPhone a hannunta.
Ba ta san cewa kafin ta isa Abuja, rayuwarta za ta iya shiga wani yanayi da ba za ta taɓa mantawa da shi ba.
Safiya yarinya ce da tun tana da shekaru 17 ta fara shiga matsala bayan ta haɗu da wasu kawayen da suka koya mata wata irin rayuwa da ba ta dace da ita ba.
Ita ce kaɗai mace da ta rage ba ta yi aure ba a gidansu.
Mahaifinta ya saki mahaifiyarta, ita kuma ta ci gaba da zama cikin gidan ba tare da kulawar uwa a kusa da ita ba.
Ta yi karatu har SS2, amma rashin mahaifiyarta a gida da yanayin rayuwar da ta shiga suka hana ta ci gaba har ta rubuta WAEC.
Sai kawayenta suka fara shigar da ita cikin rayuwar gantali, yawo da bin maza, kullum burinsu ya shine ina za mu je mu hole?
A hankali, Safiya ta fara ganin rayuwar kawayenta a matsayin abin koyi.
Har ta kai shekara 19, sai wata sabuwar damuwa ta kama zuciyarta:
“Ni ma yaushe zan mallaki iPhone?”
Wata rana kawarta Hasana ta dawo daga Abuja.
Amma ba abin da Safiya ta gani ya fi ɗaukar hankalinta kamar sabuwar iPhone da kuma ɗumbin kuɗin da Hasana ke ɗauke da su ba.
Safiya ta kalle ta da mamaki:
“Hasana, a ina kika samu sabon iPhone da waɗannan kuɗin haka?”
Hasana ta yi murmushi.
“Ai daga Abuja nake. Idan kina so, mu je tare. Ke ma za ki dawo da naki.”
Wannan magana ta isa ta canza tunanin Safiya.
“Eh wallahi, zan je.”
Bayan kwana biyu, Safiya ta shirya kamar wadda ta samu tikitin aikin Hajji.
Ranar tafiya, Hasana ta kira ta da safe:
“Kin shirya?”
Safiya ta amsa:
“Tun jiya da dare na gama shiri. Wallahi ban ma yi barci ba.”
Suka haɗu a tashar gidan mai, suka kama hanya zuwa Abuja.
Hasana har ta kira Alhaji, mutumin da za su sauka a wajensa, ta tabbatar masa suna kan hanya.
Komai yana tafiya kamar yadda aka tsara.
Har sai da motar ta bar kauyen Jos.
A lokacin da Safiya da Hasana suke zaune a kujerar baya, direban ya hangi wani abu a tsakiyar hanya.
Sai ya yi wani gagarumin salati.
Safiya ta ɗaga kai cikin firgici.
Abin da ta gani a gaba shi ne abu na ƙarshe da ta yi tsammanin zai iya faruwa a wannan tafiya.
Me direban ya gani? Kuma me ya sa Hasana ta yi shiru kwatsam?
Part 2 zai bayyana abin da ya faru a wannan hanya zuwa Abuja.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button