Siyasa

SSA Atiku Isah Ya Samu Yabo Kan Rawar Da Ya Taka Wajen Tallafa Wa Matasa A Mulkin PDP

Muna amfani da wannan dama wajen yaba da godiya ta musamman ga SSA Atiku Isah bisa kokarinsa, jajircewarsa da kuma tsantsar kishin aiki, inda ya bambanta kansa ta hanyar hidima ta gaskiya da shugabanci mai tasiri.
Duk da kasancewarsa daya daga cikin dimbin masu rike da mukamai a karkashin gwamnatin jam’iyyar PDP ta Mai Girma Gwamna, Sanata Bala Mohammed, Atiku Isah ya nuna cewa jajircewa da hangen nesa na gaskiya na iya kawo gagarumin sauyi, ko da a cikin karamin matsayi.
Baya ga ayyukansa na hukuma a matsayin Babban Mataimaki na Musamman (SSA), ya dauki matakai na musamman wajen tallafa wa matasa ta hanyar daukar wasu daga cikinsu aiki a matsayin Mataimakan Musamman a ofishinsa.
Wannan mataki ba kawai ya samar da damammaki ba, har ma ya kara wa matasa kwarin gwiwa, hadin kai da jin cewa su ma suna da muhimmanci, abin da ya sanya wannan aiki nasa ya cancanci yabo da koyi.
Muna amfani da wannan dama wajen karfafa gwiwar SSA Atiku Isah da ya ci gaba da wannan kyakkyawan aiki, tare da jawo hankalin Babanmu Mai Girma Gwamna, Senator Bala Abdulkadir Mohammed, kan irin namijin kokarin da yake yi. Ayyukansa sun dace da ginshikan shugabanci nagari da mulki mai anfani ga al’umma.
Haka zalika, muna kira ga sauran masu rike da mukaman siyasa da su dauki darasi daga wannan kyakkyawan misali ta hanyar amfani da mukamansu wajen inganta rayuwar ‘yan jam’iyya, magoya baya da al’umma baki daya.
Hakika, mulki hidima ce, kuma SSA Atiku Isah ya nuna karara abin da za a iya cimmawa idan aka hada dama da jajircewa ta gaskiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button