Siyasa

PDP Ta Musanta Jita-Jitar Cewa Gwamnan Bauchi Na Shirin Sauya Sheƙa

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Bauchi ta yi watsi da rahotannin da ke cewa Gwamnan jihar, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, na shirin ficewa daga jam’iyyar zuwa African Democratic Congress (ADC), tana mai bayyana su a matsayin ƙarya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, reshen jam’iyyar PDP na jihar ya ce zargin ba shi da tushe, yana kuma ƙoƙarin yaudarar jama’a tare da haddasa tashin hankali na siyasa ba tare da dalili ba.

Sanarwar, wadda Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Bauchi, Pharm. Sama’ila Adamu Burga (Sarkin Noman Bauchi), ya rattaba wa hannu, ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa musamman a shafukan sada zumunta.

Jam’iyyar ta ce babu ko kaɗan gaskiya a cikin ikirarin cewa Gwamna Bala Mohammed na shirin barin PDP, tana mai jaddada cewa gwamnan na nan daram a matsayin mamba mai biyayya da jajircewa ga jam’iyyar.

A cewar sanarwar, “Jagorancin jam’iyyar na sake tabbatar da cikakken goyon baya da biyayya ga Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed.”

Jam’iyyar ta kuma buƙaci al’ummar Jihar Bauchi da sauran jama’a su yi watsi da jita-jitar, tare da dogaro da sahihun hanyoyin samun labarai wajen bibiyar al’amuran siyasa a jihar.

PDP ta gargaɗi jama’a kan yaɗa rahotannin da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, tana mai cewa irin waɗannan labarai na iya kawo cikas ga kwanciyar hankalin siyasa da kuma karkatar da hankali daga harkokin mulki.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button