HOTUNA: Jagororin ECWA Bauchi South DYC Sun Kaiwa Daure David Ziyaran Jaje
Daure David ya tarbi jagororin ECWA Bauchi South DYC yayin da suka kawo masa ziyaran jaje dan gane da tsareshi da akayi a gidan kaso kwanakin baya.
Andrew Victor shi ya jagoranci ziyaran tareda sauran mambobin EXCOs na cocin.
Wannan ziyara ya nuna alaman soyayya da kauna da suke gwadawa Daure David ganin yanda yake tallafawa ta bangare da dama cikin al’umma.
Ga Abinda Ya Rubuta A Shafinsa ⇓
A yau, na samu girmamawa wajen karɓar jagorancin ECWA Bauchi South DYC, ƙarƙashin jagorancin Andrew Victor, tare da mambobin EXCOs, waɗanda suka kai mini ziyarar jaje kan tsare ni da aka yi a baya, tare da yin addu’a tare da ni.
Ina matuƙar godiya bisa ƙauna, goyon baya da kuma kyakkyawan nunin haɗin kai da aka nuna a wannan lokaci mai wahala.
Addu’o’inku da tallafawarku sun yi matuƙar muhimmanci a gare ni da iyalina.
Na gode ƙwarai, Allah Ya saka da alheri.
Hotuna Daga Bisani





