Labarai

Anthony Joshua Ya Tsira Daga Mummunan Hatsarin Lagos–Ibadan Bayan Ya Sauya Kujera, Direba Ya Bayyana A Kotu

Tsohon zakaran damben duniya a matakin World Heavyweight, ɗan asalin Birtaniya da Nijeriya, Anthony Oluwafemi Olaseni Joshua, ya tsallake rijiya da baya bayan da ya kusa rasa ransa sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a babbar hanyar Lagos–Ibadan, ɗaya daga cikin hanyoyin zirga-zirga mafi cunkoso a Nijeriya da ke haɗa Jihar Lagos da Jihar Ogun.

Rahotanni sun nuna cewa Joshua ya tsira ne bayan ya sauya wurin zama a cikin motar jim kaɗan kafin hatsarin ya faru.

Wannan mummunan lamari, wanda ya faru a ranar Litinin, ya yi sanadin rasuwar mutane biyu daga cikin na kusa da tauraron damben.

An bayyana su da Ayodele Kelvin Olu, ɗan asalin Nijeriya–Birtaniya mai shekaru 36, da kuma Gami Sina, ɗan asalin Birtaniya mai shekaru 36.

Wasu fasinjojin motar sun samu raunuka daban-daban, ciki har da Anthony Joshua da kansa, wanda daga bisani aka kai asibiti inda aka yi masa jinya, sannan aka sallame shi.

Rahoton Labaranyau ya ce bayanan sun fito ne a yayin shari’ar da ake yi a wata kotu a Jihar Ogun, a kudu maso yammacin Nijeriya, inda aka gurfanar da direban motar Lexus SUV da ke ɗauke da Joshua, mai suna Kayode Adeniyi, ɗan shekara 46, kan tuhume-tuhume da dama da suka shafi hatsarin.

A cewar bayanan da lauyan direban, Olalekan Abiodun, ya gabatar a gaban kotu, tun farko Anthony Joshua yana zaune ne a kujerar gaba ta gefen fasinja lokacin da suka tashi daga Lagos, cibiyar kasuwancin Nijeriya.

Sai dai daga baya direban ya bukaci Joshua ya koma kujerar baya saboda matsalar gani.

“Abokin aikina ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa. Abin da ya faru hatsari ne. Ban samu cikakkiyar damar tattaunawa da shi ba tukuna, amma ya bayyana cewa birkin motar ne ya gaza aiki,” in ji lauyan.

Ya kara da cewa, “Na fahimci cewa sun tashi ne daga Lagos, kuma da farko Anthony yana zaune a gaba. Amma direban ya bukace shi da ya sauya wuri saboda girman jikinsa ya hana shi ganin madubin gefe yadda ya kamata.

Saboda haka ya koma kujerar bayan direba.

Daga abin da na fahimta, Latif ne ya koma gaba bayan sun sauya wurin zama da Anthony.”

Kayode Adeniyi, wanda ake cewa ya shafe sama da shekaru uku yana aiki a matsayin direban Anthony Joshua, ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa lokacin da ya bayyana a gaban kotu, sanye da bakar riga ta Musulunci, yayin da ’yan uwansa ke sa ido kan shari’ar.

Tuhume-tuhumen da ake masa sun haɗa da tuki cikin haɗari da ya yi sanadin mutuwa, tuki ba tare da taka-tsantsan ba, sakaci wajen tuki, da kuma tuki ba tare da lasisin tuki mai inganci ba, laifuffuka da ake cewa sun sabawa dokokin Federal Highway Act na Nijeriya.

A wajen kotu, ɗan direban mai shekaru 19, Ifeoluwa Adeniyi, ya kare mahaifinsa a bainar jama’a, yana mai cewa hatsarin ba sakamakon sakaci ba ne, illa matsalar na’ura.

“Babanmu ba mai gudu ba ne. Yana bin iyakar gudu, amma sai birki ya gaza aiki. Ya yi ƙoƙarin kaucewa wata babbar mota da ke gefen hanya, amma ya buge ta,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Shekaru uku kenan yana tuka wa Anthony mota. Direba ne nagari. Da suka tashi daga Lagos, Anthony yana zaune a gaba, amma mahaifina ya bukace shi ya koma baya saboda yana toshe masa gani.”

Ya kuma bayyana cewa tafiyar na dab da ƙarewa lokacin da hatsarin ya faru, inda suka nufi Sagamu, wani muhimmin gari a Jihar Ogun, domin ziyartar ’yan uwa bayan sun ɗauko su daga filin jirgin sama.

A halin da ake ciki, Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ogun ta tabbatar da cewa direban na ci gaba da kasancewa a tsare, yayin da bincike kan musabbabin hatsarin ke gudana.

“Direban motar Lexus da ke da alaƙa da hatsarin Anthony Joshua na nan a tsare. Bincike na ci gaba,” in ji jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Oluseyi Babaseyi.

Kotu ta bayar da belin direban a kan kuɗin naira miliyan biyar, tare da mutane biyu masu tsaya masa, sannan ta ɗage shari’ar zuwa Talata, 20 ga Janairu, 2026, domin fara sauraron karar.

A wani ci gaba makamancin haka, gwamnatocin Jihar Lagos da Jihar Ogun sun tabbatar a ranar Laraba cewa an sallami Anthony Joshua daga asibiti bayan samun kulawar lafiya sakamakon raunukan da ya samu a hatsarin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button