Iyalan Wani Malamin Musulunci Daga Zariya Na Neman Taimako Bayan Ya ɓace A Abuja
Iyalan Sheikh Khalifa Sani Abdulkadir, wani sanannen malamin addinin Musulunci daga Zariya a Jihar Kaduna, sun bayyana damuwa kan ɓacewarsa bayan kwana 25 da ya tafi Abuja.
Rahotanni sun ce malamin ya bar gida ne domin warware matsalar toshe asusun bankinsa da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta yi, wanda ya shafi wani mu’amala ta kuɗi na naira miliyan biyu.
Jaridar Labaran Yau ta rawaito cewa ɗan malamin ne ya raka shi zuwa ofishin EFCC, inda daga bisani aka ce an mika lamarin ga hukumomin soja domin ci gaba da bincike.
Iyalan sun ce har yanzu ba su samu wata hulɗa kai tsaye da Sheikh ɗin ba tun bayan tsare shi a farko.
Duk da cewa an ji jita-jitar da ke danganta kamun nasa da yin addu’o’i ga wasu ‘yan siyasa, iyalan sun ce ba a sanar da su wata tuhuma a hukumance ba.



