Labarai

Gwamna Bala Ya Gargadi Sarakunan Gargajiya da Cibiyoyinsu Kan Taimaka Wa..

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya fitar da kakkausar gargadi ga sarakunan gargajiya da cibiyoyinsu kan yin duk wani yunkuri na hada baki da ‘yan ta’adda, inda ya jaddada cewa irin wadannan ayyuka na barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.

Governo Bala And Sarakuna
Governo Bala And Sarakuna

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar bakuncin Sarkin Duguri, Alhaji Adamu Muhammadu, a gidansa na mahaifa da ke Yelwan Duguri.

A nan ne ya nanata muhimmiyar rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen tattara bayanan sirri, bada gargadin gaggawa, da kuma kula da tsaron al’umma a matakin ƙasa.

Gwamna Mohammed ya yaba wa al’ummar Duguri da makwabtansu bisa yadda suke ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya, inda ya bayyana yankin a matsayin abin koyi na hadin kai, juriya, da kyakkyawar zamantakewar al’umma.

Yayin da ya sake tabbatar da kudurin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin Jihar Bauchi, Gwamnan ya jaddada cewa tabbataccen tsaro mai dorewa ba zai samu ba sai da karfaffen hadin gwiwa tsakanin gwamnati, cibiyoyin gargajiya, da al’umma baki daya.

Sai dai kuma ya bukaci mazauna jihar da su rungumi harkar noma a matsayin hanya ta karfafa tattalin arziki, inda ya tabbatar musu da goyon bayan gwamnati ta hanyar samar da ingantattun kayayyakin noma da sauran tallafin noma.

A nasa jawabin, Sarkin Duguri, Alhaji Adamu Muhammadu, ya nuna godiyarsa ga Gwamna Mohammed bisa kyakkyawar tarba da aka masa, tare da alkawarin ci gaba da ba da gudunmawar masarautarsa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da ci gaban al’umma.

Ya kuma bayyana cewa ziyarar ta zo ne domin maraba da Gwamnan zuwa gida tare da taya shi murna yayin da yake sake haduwa da iyali da abokan arziki.

Hotuna Daga Bisani

Governo Bala And Sarakuna
Governo Bala And Sarakuna
Governo Bala And Sarakuna A Duguri
Governo Bala And Sarakuna A Duguri
Governo Bala Sarakuna A Duguri
Governo Bala Sarakuna A Duguri
Governo Bala Sarakuna A Duguri
Governo Bala Sarakuna A Duguri

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button