Ƙungiyoyi Na Zargin Gwamnatin Tarayya Da Raunana Dimokuraɗiyya Da Shugabanci a Bauchi
Wasu ƙungiyoyin farar hula da na wayar da kan jama’a a Jihar Bauchi sun zargi Gwamnatin Tarayya da ɗaukar matakai da ka iya raunana dimokuraɗiyya da nagartaccen shugabanci a jihar, biyo bayan kama da gurfanar da Kwamishinan Kuɗi da Ci Gaban Tattalin Arziki na jihar, Yakubu Adamu, da Hukumar EFCC ta yi.
Ƙungiyoyin sun bayyana wannan zargi ne a ranar Litinin yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a Bauchi, wanda Ƙungiyar Jakadun Yakubun Bauchi (Yakubun Bauchi Ambassador’s Forum), Kaura Independent Communication da Yakubu Adamu Influencers suka shirya tare.
Daure David ne ya karanta sanarwar haɗin gwiwar.

A cewar ƙungiyoyin, yadda EFCC ta gudanar da shari’ar ya nuna cin zarafin tsarin doka, inda suka ce kama da gurfanar da Kwamishinan, tare da wasu manyan ma’aikatan gwamnati, na da alaƙa da siyasa kuma an yi shi ne domin raunana gwamnatin Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed.
Sun ce Kwamishinan bai aikata wani laifi ba, suna mai jaddada cewa dukkanin matakan kuɗaɗen da Ma’aikatar Kuɗi ta ɗauka an yi su ne bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki, hanyoyin aiki da gwamnati ta amince da su, da kuma dokokin kula da harkokin kuɗi da ke aiki.
Ƙungiyoyin sun kuma nuna damuwa kan yadda ake yawan ambaton sunan Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed a cikin takardun tuhuma, inda suka ce hakan ya sabawa Sashe na 308 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, wanda ke ba wa gwamna mai ci kariya daga gurfanarwa a kotu.
Sun yi watsi da zarge-zargen da suka shafi tallafa wa ta’addanci da kuma wanke kuɗaɗe, suna mai cewa ba su da tushe balle makama.
A cewarsu, babu wata ƙungiyar ta’addanci ko wani aikin ta’addanci da aka danganta da shari’ar, kuma babu wata sahihiyar hujja da aka gabatar a bainar jama’a.
Duk da goyon bayan da suka nuna ga yaƙi da cin hanci da rashawa, ƙungiyoyin sun gargaɗi EFCC da ta tabbatar tana aiki ne cikin iyakar doka, tare da gujewa duk wani zargi na amfani da hukumar wajen cin moriyar siyasa.
Sun ce aiwatar da adalci bisa son rai kaɗai na iya rage amincewar jama’a ga hukumomin yaƙi da cin hanci da kuma raunana dimokuraɗiyya.
Ƙungiyoyin sun bayyana ƙwarin gwiwa ga jagorancin Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed, inda suka ce jihar na ci gaba da samun kwanciyar hankali da kuma cigaba a fannonin ilimi, lafiya da ababen more rayuwa.
A nata jawabin, Jamila Aliyu, mamba a jam’iyyar APC, ta ce duk da cewa ba ta da ra’ayi ɗaya da masu shirya taron a siyasa, tana goyon bayan matsayinsu, tana mai zargin Gwamnatin Tarayya da nuna son kai da hukunci na siyasa.
A ƙarshe, Abdullahi Shitu na ƙungiyar Yakubu Adamu Influencers ya ce taron manema labaran na da nufin isar da abin da ya kira “muryar gaskiya” a Bauchi, yana mai jaddada cewa al’ummar jihar na tsayawa tsayin daka wajen kare dimokuraɗiyya ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba.
Ƙungiyoyin sun yi kira ga Ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya da ya sake duba shari’ar, tare da buƙatar EFCC ta cire sunan gwamnan daga dukkanin takardun tuhuma. Sun kuma gargaɗi cewa ci gaba da matakan da ake ɗauka kan gwamnatin Jihar Bauchi na iya zama barazana ga dimokuraɗiyya da tsarin mulki.
Sanarwar ta samu sa hannun Daure David a madadin Yakubun Bauchi Ambassador’s Forum, Abdul Rahman Prince Doze a madadin Kaura Independent Communication, da kuma Abdullahi Shitu a madadin Yakubu Adamu Influencers.
Ga Hotuna Daga Bisani




